Taron shawarwarin da aka yi a tsakanin kasashen shida da batun nukiliyar kasar Iran ya shafa da kasar Iran zagaye na uku ya fara a birnin Vienna daga yau Talata 8 zuwa Laraba 9 ga wata, inda bangarorin da abin ya shafa za su tattauna game da yarjejeniyar batun nukiliyar kasar Iran daga dukkan fannoni.
Haka kuma Hong Lei ya yi bayani a taron manema labaran da aka yi a wannan rana cewa, kasar Sin na fatan bangarorin da abin ya shafa za su nuna fahimtar juna tare da cimma matsayi daya kan karin batutuwan da za'a tattauna a kai ta yadda za a samu ci gaba.
Ya kuma tabbatar da cewar Kasar Sin za ta ci gaba da dukufa wajen ba da taimakon da ya dace na ganin an warware batun. (Maryam)