Ashton ta bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na hadin gwiwa da ministan harkokin wajen kasar Mohammad Javad Zarif a birnin Tehran. Ta ce kwarya-kwaryar yarjejeniyar da aka cimma da kasar tana da muhimmanci.
Ta ce ko da yake, akwai matukar wahala kafin a cimma yarjejeniya ta karshe da kasar ta Iran, kuma babu tabbas cewa za a kai ga cimma hakan. Amma tana fatan hakan za a samu tare da goyon bayan 'yan kasar ta Iran da kuma al'ummomin kasa da kasa.
A nasa bangaren, Zarif ya bayyana kudurin kasarsa na warware batun nukuliyar kasar, yana mai cewa, hakan ya dogara ga yunkurin sauran bangarorin da abin ya shafa na warware wannan matsalar a kan teburin sassantawa. (Ibrahim)