Shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya na kasar Iran (AEOI) Ali Akbar Salehi ne ya bayyana hakan, inda ya ce, an samu kyakkyawan ci gaba a tattaunawar da aka yi ta baya-bayan tsakanin Iran da kasashen nan 6 da batun nukiliyar kasar ta Iran ya shafa a Vienna, babban birnin kasar Austria.
Manufar taron da aka gudanar a birnin na Vienna daga ranar 5 zuwa 7 ga watan Maris, ita ce cimma yarjejeniya ta karshe game da shirin nukiliyar kasar ta Iran da ake takaddama a kai, bayan da aka cimma kwarya-kwaryar yarjejeniya tsakanin Iran da kasashe shida da batun ya shafa da kuma kasar Iran din kanta a ranar 24 ga watan Nuwamban shekarar 2013.
Don haka Salehi ya bukaci manyan kasashen duniya, da su yi amfani da wannan dama ta tattaunawa wajen warware kiki-kakar da ke tsakanin kasashen yamma da Iran game da shirinta na nukilya.
An dai shirya Ashton za ta gana da shugaban kasar ta Iran,ministan harkokin wajen kasar da kuma shugaban majalisar dokokin kasar a yayin da take ziyara a Tehran. (Ibrahim)