Rahoton ya kuma ce kasar ta Iran ta fara gudanar da yarjejeniyar da aka cimma a matakin farko tun daga ranar 20 ga watan Janairun da ya shude, wanda ya hada da batun tsayar da sarrafa tataccen sinadarin Uranium, da fara gudanar da aikin surka tataccen sinadarin, wadanda yawansa ya kai kilogiram 196.
Rahoton ya bayyana cewa, matakin da kasar Iran ta dauka, da kuma karin alkawarin da ta yi, sun nuna goyon bayanta ga batun, duk da cewa akwai abubuwa da dama da ya dace ta aiwatar domin warware dukkan muhimman batutuwan da suka shafi nukiliyarta.
A dai wannan rana, bangarorin nan shida, da kasar ta Iran sun kammala shawarwari tsakaninsu, na warware batun nukiliyar kasar a zagaye na farko cikin kwanaki uku a birnin Vienna. Inda a yayin taron suka cimma matsayi guda, kan tsarin da za a bi wajen aiwatar da shawarwarin a nan gaba, tare da tabbatar da jadawalin shawarwarin cikin watanni hudu masu zuwa. (Maryam)