Sakamakon tashe-tashen hankula dake wakana a kasar Ukraine, ana sa ran kammala shawarwarin da kasashen nan shida, wato Amurka, da Ingila, da Faransa, da Rasha, da Sin, da kuma Jamus ke yi tare da Iran, kan matsalar nukiliyar kasar ta Iran cikin gajeren lokaci.
Bisa rahotannin baya bayan nan, ana fatan kammala taron na birnin Vienna babban birnin kasar Austira a ran Alhamis din nan, wato kafin ranar da a baya aka tsara rufewa.
A ranar Alhamis din nan ne ake fatan babbar wakiliyar kungiyar EU mai kula da harkokin diplomasiyya da tsaro, wadda kuma ke shugabantar shawarwarin Madam Catherine Ashton, za ta halarci taron gaggawa da aka shirya a Brussel, don tattaunawa kan halin da ake ciki a kasar Ukraine, lamarin da ya janyo kammala shawarwarin birnin Vienna cikin sauri.
An ce Madam Ashton, da ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif, za su kira wani taron manema labaru bayan kammala shawarwarin. An dai fara zagayen shawarwarin na wannan karo ne a ranar 18 ga wata, a matsayin ci gaba kan shawarwarin da aka yi cikin watan Nuwambar bara.
Babban burin da kuma aka sa gaba a wannan karo shi ne, aiwatar da yarjejeniyar da aka daddale yayin shawarwarin zagaye na farko, na ranar 20 ga watan Janairun da ya gabata a birnin Geneva. Tare da kuma kokarin aiwatar da wani shiri na warware matsalar nukiliyar Iran din cikin dogon lokaci. (Danladi)