Cikin sanarwar, kwanitin sulhu ya jadadda cewa, kamata ya yi a yiwa wadanda suka gudanar, da shiryawa, da ba da taimakon kudi, da kuma goyon bayan wannan harin ta'addanci hukunci, a sa'i daya kuma, kwamitin ya bukaci kasa da kasa da su yi hadin gwiwa da gwamnatin kasar Afghanistan, bisa dokokin duniya da ka'idojin da kwamitin sulhu ya tsara, dangane da lamarin.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, kwamitin sulhu na mai da hankali sosai kan barazanar da 'yan kungiyar Taliban, da na al-Qaeda, da dai sauran kungiyoyin 'yan tawayen ke kawowa jama'ar kasar Afghanistan, da rundunonin sojojin tsaron kasar, da rundunonin sojojin kasashen duniya da ke kasar, har ma da sauran kungiyoyin ba da taimako ga kasar.
Kwamitin sulhu ya sake jadadda cewa, bisa ka'idojin MDD, kwamitin sulhu zai tsaya tsayin daka wajen yin yaki da 'yan ta'adda da za su kawo barazana ga yanayin zaman lafiya da tsaron kasa da kasa.
Ran 3 ga wata, an samu wani harin kunar bakin wake a lardin Farah, da ke yammacin kasar Afghanistan, wanda ya haddasa mutuwar mutane guda 49, ciki har da masu kai harin guda 5, yayin da kuma a kalla mutane 90 suka ji rauni.
Kungiyar Taliban ta kasar Afghanistan ta sanar da daukar alhakin harin. (Maryam)