Yayin da yake jawabi ta kafar talebijin din kasar, Hamid Karzai ya nuna cewa, a ranar 9 ga wata, 'yan kungiyar ta Taliban sun kai hari ga ma'aikatar lura da harkokin tsaron kasar da lardin Khost, don tabbatar da cewa, idan babu sojojin kasashen ketare da ke kasar, lamarin zai iya haddasa tabarbarewar yanayin tsaron kasar, ta yadda kuma zai kawo wa sojojin kasar Amurka hujjar ci gaba da kasancewa a kasar ta Afghanistan.
Amma daga bisani, kwamandan sojojin Amurka da ke Afghanistan, Joseph Dunford, ya musanta dukkan zargin da Hamid Karzai ya yi, inda ya nuna cewa, maganar ba ta da tushe ko kadan.
Bugu da kari, bisa labarin da aka samu, Hamid Karzai zai gana da sabon ministan tsaron kasar Amurka Chuck Hagel, wanda ke ziyarar aiki a kasar tasa, sai dai an soke taron ba da hadaddiyar sanarwar bangarorin biyu bisa dalilai masu alaka da tsaro. (Maryam)