A daren ranar 28 ga wata, Cameron ya kai ziyarar ba zato a kasar ta Afghanistan, inda ya duba hafsoshi da sojojin kasar Ingila dake jihar Helmand a kudancin kasar, daga baya ya tashi zuwa birnin Kabul, babban birnin kasar.
A gun taron manema labaru da Cameron da shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai suka gudanar a ranar 29 ga wata, Cameron ya bayyana cewa, kasarsa tana da shirin rage sansanin sojojin kasar dake Afghanistan zuwa wani adadi tsakanin 4 zuwa 10 bayan shekarar 2014, amma bai bayyana yawan sojojin kasar tasa da za su ci gaba da zama a kasar Afghanistan ba. (Zainab)