in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnatin Afghanistan ta ce tana son yin shawarwarin shimfida zaman lafiya da kungiyar Taliban
2013-06-24 10:43:18 cri
A ran 23 ga wata, wani jami'in gwamnatin kasar Afghanistan ya bayyana cewa, muddin bangarori daban daban na masu ruwa da tsaki za su iya tabbatar da matsayin siyasa ga ofishin kula da harkokin shawarwari na kungiyar Taliban, to, ba shakka gwamnatin Afghanistan za ta shiga shawarwarin kawo zaman lafiya a tsakaninta da ragowar sansan.

A yayin taron manema labaru da aka yi, malam Janan Musazai, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Afghanistan ya ce, za a iya yin amfani da ofishin kungiyar Taliban dake kasar Afghanistan, da aka bude a birnin Doha na kasar Qatar kwanan baya wajen yin mu'ammala kai tsaye da yin shawarwarin tabbatar da zaman lafiya, kuma bai kamata a yi amfani da shi domin sauran harkokin siyasa ba. Ya ce, idan za a iya amincewa da wannan sharadi, gwamnatin Afghanistan za ta tura tawagar wakilanta zuwa birnin Doha domin halartar shawarwarin kawo zaman lafiya.

A ranar 18 ga wata, kungiyar Taliban ta kasar Afghanistan ta yi shelar bude ofishinta a birnin Doha na kasar Qatar. Har ila yau akwai jami'in gwamnatin kasar Amurka da ya tabbatar da cewa kasarsa za ta yi shawarwari da kungiyar Taliban kai tsaye, lamarin ya sa gwamnatin kasar Afghanistan nuna rashin amincewa da hakan. A ranar 19 ga wata, shugaba Hamid Karzai na kasar Afghanistan ya sanar da dakatar da aikin yin shawarwari kan "yarjejeniyar tsaron kai tsaye tsakanin kasashen Afghanistan da Amurka", kuma ya soke shirin tura mambobin kwamitin zaman lafiya na kasar zuwa birnin Doha. Bugu da kari sakamakon sukan da gwamnatin kasar Afghanistan ta yi da kakkausar harshe, babu sauran hanyar da za a iya bi, illa a dakatar da shawarwarin kawo zaman lafiya karo na farko da ya kamata a ce an fara tsakanin bangaren Amurka da kungiyar Taliban a ranar 20 ga wata. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China