Shugaban Afghanistan ya ba da umurnin fitar da sojojin musamman na Amurka daga kasar
A ranar Lahadi 24 ga wata, shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai, ya ba da umurni ga ministan kula da harkokin tsaron kasar, na fidda dukkan sojojin musamman na kasar Amurka daga jihar Vardak da ke tsakiyar kasa cikin makonni guda biyu masu zuwa. Dalilin haka shi ne domin wasu daga cikinsu sun rika muzgunawa mazaunan wurin tare da kashe wasunsu, lamarin da ya haddasa tashin hankali, tare da kawo barazana ga yanayin tsaron yankin. (Maryam)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku