Ranar 13 ga wata, ta bakin kakakinsa, Ban Ki-Moon ya ba da sanawar yin tir da harin da aka kaiwa wurin dake dab da kotun koli a birnin Kabul hedkwatar kasar Afghanistan a yammacin ranar 11 ga wata.
Sanarwar ta ce, wannan harin kunar bakin wake da Taliban ta aiwatar ya haddasa asarar rayukan fararen hula da dama, inda Ban Ki-Moon ya yi Allah wadai da lamarin sosai tare kuma da nuna juyayi ga iyalan mamatan.
Ban Ki-Moon ya nanata cewa, bai yarda a kai hari kan fararen hula ba, domin ya sabawa dokar jin kai ta kasa da kasa, kana ya yi kira ga wadanda suka aikata laifin da su daina kai irin wannan harin dake kawo wa jama'ar Afghanistan wahalhalu sosai.
'Yan sandan kasar sun bayyana a ran 11 ga wata cewa, harin da aka kai a wannan rana da yamma, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a kalla 12, yayin da wasu 30 suka raunata. Taliban ta sanar da daukar alhakin aiwatar da harin, da zummar kai hari kan kotun koli. (Amina)