in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hamid Karzai ya ce shugaban kungiyar Taliban zai iya halartar babban zaben kasar Afghanistan
2013-04-03 17:10:22 cri
Shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai ya bayyana a Talata 2 ga wata cewa, shugaban kungiyar Taliban, Mullah Mohammad Omar, zai iya halartar babban zaben kasar na shekarar 2014 a matsayin dan takara. Zaben zai zama irinsa na 3 da ya gudana a kasar Afghanistan bayan rushewar gwamnatin Taliban a shekarar 2001.

Kafofin watsa labarun kasar Afghanistan sun ruwaito cewa, a hirar Shugaba Hamid Karzai da wakilin wata jaridar kasar Jamus a ranar 2 ga wata, ya ce tsarin mulkin kasar ya bai wa dukkan 'yan kasar damar halartar babban zabe, don haka shugaban kungiyar Taliban shi ma zai iya shiga zaben..

Yayin da Mista Karzai ya ziyarci kasar Qatar a kwanakin baya, ya yi musayar ra'ayi da shugaban kasar Qatar kan yadda kungiyar Taliban za ta kafa wani ofis a kasar, lamarin da aka bayyana cewa shugabannin bangarorin 2 sun riga sun cimma ra'ayi daya, sai dai an jaddada cewa aikin ofishin da za a kafa ya tsaya kan shawarwarin sulhuntawa tsakanin bangarorin kasar Afghanistan kawai. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China