A cewar Ashraf Ghani Ahmadzai, shugaban hukumar da ke sa-ido kan shirin mika harkokin tsaro ta wucin gadi a wani biki, wanda ya samu halartar dakarun Afghanistan da na NATO wanda aka yi a hedkwatar gundumar Bazarak, za a kashe kusan dala biliyan 20 wajen karfafa dakarun Afghanistan cikin shekaru 3 masu zuwa, yana mai karawa da cewa, za a yi amfani da sama da dala miliyan 30 cikin wannan adadi wajen taimakawa 'yan sanda da sojoji da ke gundumar Panjshir
Ya zuwa yanzu gwamnatin Afghanistan ta karbi ikon kula da harkokin tsaro a gundumar Bamyan, da garuruwan Mazar-e-Sharif Mehterlam, Lashkar Gah, da Herat. (Ibrahim)