in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ba ta samu shaidar kai tsaye ta faduwar jirgin saman Malaysia ba
2014-03-27 16:12:27 cri

Kakakin ma'aikatar zirga-zirga da jigila ta kasar Sin Mista Li Yang, ya bayyana cewa, kawo yanzu kasar Sin tana burin samun kayayyakin da ake tantama a kansu, kasancewar babu wata shaidar kai tsaye, da ta tabbatar da faduwar jirgin saman kasar Malaysia mai lambar MH370 cikin teku. Ana kuma hasashen gudanar da aikin ceto cikin dogon lokaci.

Li wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis din nan a birnin Beijing, ya ce jiragen ruwa 12 na kasar Sin, suna gudanar da aikin lalube a kudancin tekun India, wadanda kuma suka zama ginshikin aikin da ake yi. A cewar sa babban aikin dake gabansu shi ne, neman tarkacen da ake zaton suna da nasaba da jirgin saman da ya bace ne.Li ya kara da cewa, sai lokacin da kasar Sin ta samu wadancan kayayyaki, za ta tabbatar da ko jirgin ya fada a teku ko a'a. Da kuma zarar an tabbatar da hakan ne, za a gudanar da nazari bisa halin da ake ciki a kudancin tekun na India, da yanayinsa, da igiyar ruwa, sa'an nan a kebe yankunan da ake bukatar gudanar da bincike a cikinsu. A kuma tsara cikakken shirin neman baraguzan jirgin, da na'urar dake nadar bayanan jirgin. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China