A ran 20 ga wata, wani jami'in hukumar tsaron tekun kasar Australia ya bayyana cewa, kasar ta gano wasu abubuwan da ka iya zama tarkacen jirgin saman Malaysia da ya bace a kudancin tekun India.
Sa'an nan kuma, jiya da yamma, kakakin wani kamfanin amfani da taurarin dan Adam wajen kasuwanci na kasar Amurka ya gaskanta cewa, kamfaninsa ya gabatar da hotunan taurarin dan Adam ga hukumar tsaron tekun kasar Australia, kuma zai ci gaba da yin bincike kan yankin tekun game da abubuwan da ka iya zama tarkacen jirgin saman Malaysia da ya bace.
Haka kuma jiragen ruwan sintiri biyu na cibiyar aikin ceto kan teku ta kasar Sin sun ci gaba da gudanar aikin bincikensu a kudancin tsibirin Christmas bisa shirin da aka tsara, kuma za su tafi yankin tekun da aka gano abubuwan da ka iya zama tarkacen jirgin saman Malaysia da ya bace. Bugu da kari, akwai jiragen sama guda biyu na kasar Sin da suka tashi zuwa wani sansanin sojojin sama na kasar Malaysia cikin gaggawa don gudanar da sabon shirin gano jirgin saman kasar Malaysian nan da ya bace. (Maryam)