Game da sabon ci gaba da aka samu dangane da jirgin sama na Malaysia da ya bace, kakakin ma'aikatar tsaron Sin Mista Geng Yansheng ya bayyana a gun taron manema labaru da aka shirya a ran 27 ga wata cewa, a halin yanzu ana ci gaba da gudanar da aikin ceto. Kasar Sin za ta tura isassun sojoji, wadanda za su yi iyakacin kokarin gudanar da aikin ceto.
Mista Geng ya ce, a yayin aikin ceto, sojojin Sin sun yi cudanya da hukumomin tsaro da sojoji na kasashen da abin ya shafa. A halin yanzu dai, sojojin ruwa da na sama na kasar Sin sun yi hadin gwiwa sosai da sojojin Australiya da Malaysia. (Danladi)