in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ba za ta daina neman jirgin saman Malaysian da ya bace ba
2014-03-24 20:41:07 cri
Kasar Sin ta ce ba za ta daina neman jirgin saman Malaysia da ya bace ba,yadda kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Hong Lei ya bayyana a taron manema labaran da aka yi a yau Litinin ranar 24 ga wata.

Mr. Hong ya ce, kasar Sin ta riga ta roki kasashen Malaysia da Australia da su kara azama game da neman jirgin saman nan a yankunan tekun da aka fi kyautata zaton fadawarsa, sannan kuma kasar na ci gaba da yin shawarwari tare da bangarorin biyu.

Bugu da kari, hotunan da kasar Sin ta riga ta gano ta tauraron dan Adam na abubuwan da ka iya zama tarkacen jirgin saman, tun da farko ta riga ta gabatar da su ga kasashen da abin ya shafa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China