in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bukaci Malaysia ta gabatar da dukkan shaidun faduwar jirgin ta
2014-03-25 10:24:55 cri

A ran 24 ga wata da dare bisa agogon wurin, firaministan Malaysia Mohammad Najib Razak, ya sanar a birnin Kuala Lumpur cewa, sakamakon nazari hotunan tauraron 'dan Adam da aka gudanar, hukumar lura da tauraron 'dan Adam ta duniya, da hukumar binciken faduwar jiragen sama ta Birtaniya, su cimma matsaya guda, cewa jirgin saman kasar da ya bace ya fada ne kudancin tekun India.

Wannan batu ya yi matukar janyo hankalin daukacin masu ruwa da tsaki, inda mataimakin ministan harkokin wajen Sin Mista Xie Hangsheng, ya yi ganawar gaggawa da Iskandar Sarudin, jakadan Malaysia da ke a Sin a ran 24 ga wata da dare.

Mista Xie ya ce, kasar Sin na bukaci Malaysia ta gabatar da dukkan shaidun faduwar jirgin, tare da cikakkiyar kididdiga da tauraron 'dan Adam, da sauran shaidun da abin ya shafa suka samar. Xie ya karfafa cewa, a halin yanzu bai kamata a daina aikin laluben jirgin ba. Kuma Sin ta bukaci Malaysia za ta ci gada da gudanar da ayyuka daban daban ciki har da na neman wannan jirgi.

Har wa yau shi ma kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Mista Hong Lei, ya bayyana cewa, kasar Sin ta riga ta mika bukatar ta ga Malaysia, ta neman dukkan bayanai da shaidu, da ke da alaka da faduwar jirgin cikin teku. A sa'i daya kuma, cibiyar kula da aikin ceto a teku ta kasar Sin tana nazarin matakin da ya dace a dauka. Kuma Sin za ta kara inganta aikin ceto, tare da kara tura jiragen ruwa zuwa kudancin tekun India don neman wannan jirgi.

Hukumar kula da aikin tsaro a kan teku ta kasar Australiya ce dai ta sanar a ran 25 ga wata cewa, an dakatar da aikin laluben wannan jirgi, sakamakon rashin kyawun yanayi.

Bisa la'akari da iska mai karfi, da ruwan sama, da karfin igiyar ruwa a tekun, ta yanke shawarar dakatar da aikin da ake yi, ya zuwa ranar 26 ga wata, lokacin da ake fatan kyautatuwar yanayin. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China