Ranar 25 ga wata da safe, Li Keqiang, firaministan kasar Sin ya shugabanci taron majalisar gudanarwar kasar dangane da ayyukan yau da kullum, inda ya saurari rahoton da aka mika masa game da batutuwan da suka shafi neman jirgin saman kasar Malaysia da ya bace, bayan da gwamnatin Malaysia ta gabatar da wasu bayanai.
Mista Li ya nuna cewa, ya zuwa yanzu neman jirgin saman shi ne aikin gaggawa da ke gaba da kome. Don haka wajibi ne hukumomin kasar Sin da abin ya shafa su bukaci Malaysia da ta kara samar da bayanai masu amfani, ta bi yarjejeniyoyin kasa da kasa yadda ya kamata, ta kuma ci gaba da rarraba ayyukan ceto yadda ya kamata a tsakanin gamayyar kasa da kasa, sannan ta gayyaci kwararrun kasar Sin da su shiga ayyukan binciken dalilin hadarin jirgin saman.
Sa'an nan kuma, Li ya bayyana cewa, dole ne dukkan sassan kasar Sin da ke gudanar da ayyukan ceto a yankunan tekun da ake zaton hadarin ya abku su ci gaba da kokarinsu na neman wannan jirgin sama, kada su gaza a kokarinsu. Yana mai tabbatar da cewa, gwamnatin Sin za ta ci gaba da daukar hakikanin matakan kiyaye halaltattun hakkokin al'ummanta.(Tasallah)