in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Malaysia ya gana da manzon musamman na Sin
2014-03-26 20:39:31 cri
Yau Laraba 26 ga wata, firaministan kasar Malaysia Najib Tun Razak ya gana da manzon musamman na gwamnatin kasar Sin, kuma mataimakin ministan ma'aikatar harkokin wajen kasar Zhang Yesui.

Yayin ganawarsu, Mr. Zhang ya bayyana cewa, muhimmin aiki a halin yanzu shi ne neman jirgin saman da ya bace, don haka ba za a tsayar da aikin bincike ba, kuma kasar Sin za ta kara himma wajen neman jirgin saman nan. Ya ce kasar Sin na fatan karfafa mu'amalar dake tsakanin kasashen biyu dangane da labaran jirgin saman da ya bace, ta yadda za a iya samun tabbataccen bayani kan faduwar jirgin saman nan a kudancin tekun India, wanda hakan zai ba da taimako matuka ga kasa da kasa wajen binciken jirgin. A cewarsa ya kamata a ba iyalan wadanda ke cikin jirgin saman nan hakuri cikin kwanciyar hankali.

A nasa tsokaci, firaministan kasar Malaysia Najib Tun Razak ya bayyana cewa, kasarsa na maraba da kuma yin matukar godiya ga kasar Sin don taimako da ta samar wajen binciken jirgin saman, sannan kasar Malaysia za ta ci gaba da dukufa wajen samar da tabbataccen bayani game da jirgin saman cikin lokaci, tare da nemansa a kudancin tekun India. Ya ce kasar za ta yi kokari kan lallashi iyalan wadanda ke cikin jirgin saman nan yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China