in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta tura tawaga ta musamman zuwa Malaysia dangane da bacewar jirgin sama
2014-03-25 20:37:10 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umurnin a tura tawaga ta musamman zuwa Kuala Lampur, babban birnin kasar Malaysia domin shiga cikin al'amuran binciken jirgin saman nan mai lamba MH370.

Bisa umurnin da Shugaban ya bayar a yau din nan Talata 25 ga wata, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Zhang Yesui zai jagoranci tawagar ta musamman zuwa Kaula Lampur nan ba da dadewa ba.

Shugaba Xi ya kuma ba da umurnin ga hukumomin gwamnatin kasar da su taimaka ma Malaysia da sauran bangarorin da ke bukatan hakan wajen neman wannan jirgin saman fasinjan da ya yi batan dabo. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China