Jarin waje a kasar Tunisia ya ja da baya da kashi 6.5 cikin 100 a farkon watanni hudu na wannan shekara ta 2013 da Dinar miliyan 549.3 kimanin dalar Amurka miliyan 333.2 idan aka kwatanta da na shekarar 2012 dake Dinar miliyan 587.6, kimanin dalar Amurka miliyan 356.4 bisa ga makamancin wannan lokaci, a cewar wasu alkaluma na baya baya na ma'aikatar bunkasa jarin wajen kasar FIPA.
A lokacin da yake hira da manema labaran gida da na waje a ranar Talata, babban darektan FIPA Noureddine Zekri ya bayyana cewa, wannan ja da baya ya zo ne sakamakon tashe-tashen hankalin da kasar take fuskanta tun farkon wannan shekara wadanda suka janyo kasha-kashen mutane tare da ba da misalin kisan gillar 'dan adawa Chokri Belaid a ranar 6 ga watan Febrairun da ya gabata da kuma rikicin ta'adanci da ake samu a kan iyaka da kasar Aljeriya.
Har zuwa karshen watan Afrilun shekarar 2013, sakamakon zuba jarin waje a kasar Tunisia ya biyo bayan niyyar dakatar da ayyuka 32 da kamfanonin waje suka dauka, kuma kashi 25 cikin 100 na dalilin da ya sa suka dauki wannan mataki na da nasaba da yanayin rashin tsaro da tabarbarewar yanayin tattalin arzikin kasar, in ji mista Zekri. A tsawon farkon watanni hudu na shekarar 2013, sabbin kamfanoni kusan talatin ne kawai suka bude a kasar Tunisia idan aka kwatanta da shekarar 2012 da aka samu sabbin kamfanoni 35 da suka bude. Hakazalika wadannan sabbin kamfanoni tare da bunkasuwarsu a tsawon watanni hudu na shekarar 2013 sun samar da ayyukan yi 1669, adadin da ya yi kasa da na shekarar da ta gabata dake 2729. (Maman Ada)