Rahotanni daga birnin Magadishu sun bayyana cewa, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun harbi wani 'dan jarida mai suna Mohamed Ibrahim Rageh a kofar gidansa, wanda ke garin Dharkenley a birnin na Mogadishu.
'Yan bindigar sun tsere bayan da suka harbi Rageh, kafin isowar jami'an tsaro da a yanzu haka ke ci gaba da bincike kan lamarin. Kuma kawo wannan lokaci, babu wata kungiya ko wani da ya dauki alhakin kisan wannan 'dan jarida. Rageh wanda ke aiki a hukumar gidajen talabijin da Radio mallakar gwamnatin kasar, shi ne mutum na 4 da aka kashe a birnin na Mogadishu a bana. Tuni dai mahukuntan kasar suka bayyana cewa, suna da alamar da za ta ba su damar cafke wadanda suka aikata wannan ta'asa.
A nata bangare, kungiyar 'yan jaridar kasar "NUSOJ", ta yi Allah wadai da kisan wannan mamba nata, tare da kira ga mahukuntan kasar, da su tabbatar da hukunta wadanda suke da hannu cikin lamarin. Masharhanta dai na kallon wannan kasa ta Somalia, a matsayin mafi hadari ga 'yan jaridu a dukkanin nahiyar Afirka, ta biyu kuma a hadari bayan kasar Sham a dukkanin fadin duniya. A bara ma dai, an hallaka 'yan jarida har 18 a kasar.(Saminu)