in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya na baiwa kamfanonin kasar Sin kwarin-gwiwa su zuba jari a kasar
2013-07-31 16:26:28 cri


Ranar Talata 30 ga wata ne, aka yi wani taron bayyana ayyukan da ministocin gwamnatin Najeriya suka gudanar a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, wanda ministan kula da harkokin masana'antu, cinikayya da zuba jari na Najeriyar Olusegun Aganga, da ministan yada labaru Labaran Maku suka halarta.

A cikin jawabinsa, Mista Olusegun Aganga ya yaba ayyukan da kamfanonin kasar Sin suke gudanarwa a Najeriya, musamman ma kamfanonin gine-gine, kamar kamfanin CCECC, wanda ya kafa wata harabar masana'antu a yankin Idu dake birnin Abuja, kana yayi hayar ma'aikata 'yan Najeriya da dama a wurin.

Sa'an nan a yankin cinikayya maras shinge na Lekki dake birnin Ikko, akwai kamfanonin kasar Sin da dama wadanda ke yin hayar ma'aikata 'yan Najeriya da yawa.

Mista Aganga ya kuma ja hankalin kamfanonin kasar Sin manya da kanana, don su zo nan Najeriya su zuba jari, saboda Najeriya na da babbar kasuwa da kuma damar yin kasuwanci. (Murtala)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China