in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Congo-Brazzaville ta kafa wani asusun kasa na zuba jari
2013-08-09 11:10:13 cri

Gwamnatin kasar Congo ta yanke shawara a ranar Alhamis a birnin Brazzaville cewa, ta kafa wata hukumar gwamnati mai halaka da harkokin tattalin arziki da kasuwanci mai sunan asusun zuba jari na kasar.

Shirin dokar kafa wannan asusu a gabar da shi a wani zaman taron ministoci a karkashin jagorancin shugaban kasar Congo Denis Sassou-N'guesso, tare da ministan kasa, ministan tattalin arziki, kudi, fasali da kuma harkokin dunkulewar Afrika, mista Gilbert Ondongo, a cewar wata sanarwar da ta biyo wannan zaman taro.

Kafa wannan asusu na da nasaba da cewa, tun yau da 'yan shekaru, hukumar kudi ta gwamnatin Congo tana kara samun kudin shiga, da za'a ce fiye da cikin shekarun da suka gabata, in ji ministan watsa labarai kuma kakakin gwamnatin kasar Bienvenu Okiemy. Kamar yadda ake yi a sauran kasashe dake samun irin wannan karin kudin shiga ta hanyar sayar da albarkatun kasa kuma ta hanyar wasu fannonin kasuwancin waje, dalilin haka ne irin wadannan kudade suke kasancewa wata dama ta ajiya ga gwamnati, in ji mista Okiemy. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China