Yankin cinikayya cikin 'yanci na Onne dake jihar Rivers a kudancin Najeriya ya samu karin jari da aka zuba masa na dalar Amurka miliyan 200 a cikin wannan shekarar, in ji gwamnatin tarayyar kasar.
Ministan masana'antu da ciniki da zuba jari Mr. Olusegun Aganga ya fadi hakan ne a wajen wani taron zuba jari a bangaren mai da iskar gas karo na biyu da aka yi a garin Onne, mai taken damar zuba jari a sassa dake binciko da hako danyan iskar gas da sarrafa su.
A cikin jawabin nasa, ya ce, ya zuwa yanzu, a bangaren yankin cinikayya cikin 'yanci na Onne kawai, wannan sakamako ya gamsar da cigaban tattalin arzikin kasar ta fuskar kalubalen da kasashen duniya ke fuskanta.
Mr. Aganga ya ce, yankin cinikayya cikin 'yanci a bangaren mai da iskar gas ya taka rawar a zo a gani kwarai, musamman ganin karin jarin da aka zuba har na dalar Amurka miliyan 200 a cikin wannan shekarar kawai a kan dalar Amurka biliyan 4 da tun da farko aka same su. (Fatimah)