in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'ummar Afirka na farin ciki da jarin Sin a nahiyar
2014-03-18 10:01:51 cri

Sakamakon wani bincike na jin ra'ayin al'umma ya nuna cewa, da yawa daga al'ummar Afirka sun gamsu, da alfanun jarin kamfanonin Sin a nahiyar.

Binciken wadda wasu cibiyoyin binciken kasar Kenya da na Afirka ta Kudu suka gudanar a bara, aka kuma fidda sakamakonsa a ranar Litinin, ya nuna yadda mutanen nahiyar ta Afirka ke bayyana imaninsu, da yanayin hada hadar kasuwancin kamfanonin Sin, baya ga karin guraben ayyukan yi da suke samarwa.

An dai gudanar da wannan bincike ne a kasashen Afirka 15, inda mafiya yawan wadanda suka bayyana ra'ayinsu, suka fito daga kasashen Afirka ta Kudu, da Najeriya da kuma Kenya.

Kasar Sin dai dake matsayi na biyu a duniya, ta fuskar bunkasar tattalin arziki, a yanzu na kara kwazo wajen zuba jari a Afirka, inda yawan jarin nata ya karu, daga dalar Amurka miliyan dubu 10 a shekara ta 2000, ya zuwa dala miliyan dubu 200 a bara. Ta kuma cika shekaru hudu da zarta Amurka, a matsayin babbar kawa ta fuskar hada hadar cinikayya da kasashen dake nahiyar ta Afirka.

'Yan kasuwar Sin wadanda ke samun goyon baya daga mahukuntan kasarsu, a yanzu na ci gaba da gogayya da sauran takwarorinsu na kasashen Japan da India, da ma na sauran manyan kasashen nahiyar Turai da Amurka, wajen zuba jari a fannonin samar da ababen more rayuwa a Afirka. Sashen da ya hada da harkokin sadarwa, da hakar ma'adanai, da ma samar da kayayyakin bukatun yau da kullum, wadanda a baya kamfanonin yammacin Turai ke kan gaba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China