Firaministan kasar Namibia Hage Geingob, ya ce, kasarsa a shirye take, ta karbi bakuncin daukacin Sinawa masu sha'awar zuwa jari.
Geingob wanda ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da ya yi da wakilin kamfanin dinlancin labarun kasar Sin Xinhua, gabanin ziyarar aiki da zai kawo nan kasar Sin, ya kara da cewa, yana fatan amfani da wannan ziyara, wajen karfafa dangantakar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin.
Ya ce, sassan kasuwanci, cinikayya da bunkasa masana'antu, na cikin fannonin da yake fatan gwamnatocin biyu za su baiwa kulawa. Matakin da a cewar sa zai ba da damar cimma moriyar juna a nan gaba.
Ana sa ran yayin ziyara da firaministan kasar ta Namibia zai gudanar a nan kasar Sin, daga ranar 4 zuwa 13 ga watan Afirilun dake tafe, zai jagoranci tawagar masana, da 'yan kasuwar kasarsa, wajen ganawa da takwarorin su na nan kasar Sin. (Saminu)