in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ce ke kan gaba a fuskar zuba jari a Zimbabwe
2013-07-03 12:22:52 cri

Cibiyar bunkasa harkokin cinikayya ta kasar Zimbabwe ta bayyana ranar Talata cewa, har yanzu kasar Sin ce babbar mai zuba jari a kasar, a cikin watanni biyar na farkon shekarar nan, inda kudi da ta zuba ya kai kashi 74 cikin dari na adadin dalar Amurka miliyan 134 na kudade da suka shigo kasar dake kudancin Afirka daga waje.

Sauran manyan masu zuba jari a Zimbabwe sun hada da kasar Mauritius wacce ta zuba jarin dalar Amurka miliyan 11 a fannin hako ma'adinai da ayyukab hidima, kana kasar Afirka ta Kudu ta zuba jari a fuskar hako ma'adinai da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 7.

Kasar Zimbabwe tana farfadowa ne daga koma bayan tattalin arziki da ta shafe shekaru 10 a ciki, wanda kuma ya kasance lokaci da aka yi fama da hauhawar farashin kayayyaki, musamman a shekarar 2008.

Bayan da hukumomin kasar suka soke amfani da dalar kasar Zimbabwe wacce ta zamo ba ta da daraja, aka kuma bullo da wasu samfurin kudade har da dalar Amurka, an samu dawowar zuba jari a kasar sannu a hankali.

A shekarar da ta wuce, hukumar zuba jari ta kasar Zimbabwe ta amince da shigo da kudaden zuba jari da yawansu ya kai dalar Amurka miliyan 929, wanda daga ciki kasar Sin ta zuba kashi 72 cikin dari. Ministan kudade na kasar Tendai Biti a cikin watan da ya gabata ya baiyana cewa, rashin tabbas dangane da batun zabe a kasar na kawo cikas ga bunkasar tattalin arzikin kasar a wannan shekara. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China