Jakadan kasar Sin dake Masar Song Aiguo a jiya Lahadi 21 ga wata ya ce, jarin da Sin ta zuba a kasar ya karu da kashi 60 a cikin 100 a shekaru 2 da suka gabata, abin da ya kai fiye da kudi dalar Amurka miliyan 500, kamar yadda wani jami'in ofishin jakadancin ya tabbatar.
A lokacin da yake rangadin wani yanki na masana'antu a Giza, jakada Song ya ce, jarin da Sin ta zuba a cikin shekaru biyu ya karu da kimanin kudi dalar Amurka miliyan 200, abin da hakan ya sa ya wuce miliyan 560 gaba daya.
A lokacin wannan rangadin da ya samu rakiyan gwamnan Giza Ali Abdel Rahman, tawagan kasar Sin din da jakadan ya jagoranta sun ziyarci babbar cibiyar masana'antu da zuba jari na Abu Rawwash dake garin Gizan.
Jakadan na Sin wanda ya bayyana sabon yankin na masana'antu a matsayin wani matakin gaba da na tattalin arziki a kasar ta Masar, ya yi fatan cewa, kasashen biyu za su fadada huldarsu da dangantaka da ke tsakaninsu kamar yadda shugabannin kasashen biyu suka dau kudurin yi.
A nashi bangaren, gwamnan Giza Ali Abdel Rahman ya yi fatan cewa, rangadin da jakadan ya kai yankin zai bude wani shafi na cigaba tare da zuba jari daga kasashen waje, yana mai tabbatar da cewa, garin Giza yana da yanayi mai kyau na zuba jari, musamman saboda yanayin inda yake da ya kunshi wuraren yawon shakatawa, masana'antu da kuma aikin noma.(Fatimah)