in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nigeriya tana neman masu zuba jari na ketare a bangaren wutar lantarki
2014-02-11 09:56:10 cri

Gwamnatin tarayyar Nigeriya ta bakin ministan wutar lantarkinta Chinedu Nebo, ta yi kira ga masu zuba jari na kasashen waje da su yi amfani da damar da ta bayar a bangaren samar da wutar lantarki domin su zuba jari.

Mr. Nebo ya yi wannan kiran ne a lokacin bude babban taron a game da wutar lantarki da daukan nauyin ababen more rayuwa da aka yi a Abuja, babban birnin kasar a ranar Litinin din nan.

Ya ce, akwai bukatar masu zuba jari su yi amfani da damar da aka bayar kwanan nan wajen sayar da hannayen jarin wassu manyan ma'aikatun kasar su zuba jari a ciki domin inganta bangaren da kuma rage karancin ababen more rayuwa inda ya yi bayanin cewa, an shirya wannan taron ne domin samar da wata dama ta cudanya da sabbin masu bukatar zuba jari da hukumomin kudin kasar domin a daidaita a inda ya kamata a wannan bangaren.

Sai dai ministan ya koku ga yadda ake kara samun matsalar fasa bututun albarkatun mai wanda yake kawo illa ga samar da iskar gas ga tashoshin wutar lantarkin kasar, sannan ya ba da tabbacin cewa, ma'aikatarsa tana iyakacin kokarinta tare da jami'an tsaro na ganin ta shawo kan wannan matsalar.

A lokacin taron, wakilan kasashen waje da masu bukatar zuba jari sama da 310 daga kasashe 29 da suka hada da hukumomin kudin na gida da na kasashen waje 50 suka halarci wannan taron. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China