in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta Kudu na fatan habaka harkokin zuba jari tsakaninta da Rasha
2013-11-29 16:19:00 cri

Rahotanni daga Afirka ta Kudu na cewa, wata tawagar jami'ai da 'yan kasuwar kasar, za ta halarci taron bunkasa cinikayya da zuba jari karo na 6, da za a yi a kasar Rasha, domin nazartar hanyoyin kara samarwa kasar kakofin zuba jari, da bunkasa kasuwanci.

A cewar kakakin sashen lura da harkokin bunkasa cinikayya da zuba jari na kasar Sidwell Medupe, Afirka ta Kudu ta dauki wannan taro da za a yi a birnin Vladivostok, tsakanin ranekun 3 zuwa 6 ga watan Disamba mai zuwa da matukar muhimmanci. Medupe ya ce, taron wanda zai mai da hankali ga tattauna batutuwan da suka shafi bunkasa harkokin zuba jari da cinikayya, zai baiwa wakilan kasarsa damar gano karin sassan da za a iya zuba jari, musamman bangaren harkokin noma da hakar ma'adanai.

Wannan taro mai lakabin ITI, kasashen Afirka ta Kudu da Rasha ne suka kirkire shi, domin ya zamo hanyar kara bunkasa harkokin da suka shafi cinikayya da zuba jari tsakanin kasashen biyu. A kuma bara, kimanin kamfanoni 28 ne suka halarce shi, lamarin da ya yi sanadiyar fidda hajojin kasar na makudan kudade, watanni 6 da kammalar taron. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China