Yayin wani taron manema labaru da aka yi a ranan Litinin 24 ga wata, Kofi ya ce kimanin masu fafutukar 20 ne daga Liberia suka tsallako tare da kaddamar da harin na ran Lahadi 23 ga wata, wanda ya rutsa da sojojin kasar 4, tare da wani mahari daya, aka kuma cafke mahara 3. Yanzu haka dai an farfado da yanayin zaman lafiya a yankin da lamarin ya auku.
A wani ci gaban kuma, an cafke dakarun sa kai na kasar Cote d'Ivoire fiye da 20, wadanda suka tsere zuwa Laberiya, a kan hanyar su ta komawa gida a mako da ya gabata, an kuma mika su ga mahukuntan Cote d'Ivoire.
Idan dai ba a manta ba, an sha samun aukuwar hare-hare a yammacin kasar Cote d'Ivoire, tun bayan kammalar babban zaben kasar a watan Afrilun shekarar 2011. Har wa yau a watan Yunin shekarar 2012, masu fafutuka sun kai wani hari kan birnin Ta'i dake yammacin iyakar kasar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye 10, ciki hadda sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD su 7. (Amina)