ONUCI na matukar mamakin wannan jita jita ta ba zata dake cigaba da yaduwa dake nuna cewa ta maido mista Charles Ble Goude a cibiyarta dake Sebroko. Tawagar MDD ta yi watsi da wannan jita jita da bata da tushe tare da bada karin hasken cewa bata taba tsare mista Ble Goude cibiyarta ba in ji kakakin ONUCI madam Kadidia Ledron a cikin wata sanarwa.
Haka kuma jami'ar ta bayyana cewa ofishinsu ba wani reshen hukumar hukunta manyan laifuffuka CPI ba ce a kasar Cote d'Ivoire kana kuma ONUCI ba tada hurumin shiga cikin harkokin shari'a na kasar.
ONUCI zata cigaba da gudanar ayyukanta cikin adalci domin karfafa zaman lafiya, sasanta 'yan kasa da kuma taimakawa yin shawarwari siyasa tsakanin bangarori daban daban na kasar in ji madam Ledron.
A kwanan ne dai wasu jaridun kasar na kusa da Laurent Gagbo da wasu shafukan internet suka watsa wani sharhi a ranar Asabar dake bayyana batun tsare mitsa Charles Ble Goude a cibiyar ONUCI dake Sebroko dake uunguwar Attecoube a birnin Abidjan lamarin dake nasaba da binciken hukumar CPI. (Maman ADA)