A cikin wata sanarwar da aka fitar a ranar Asabar, ministan tsaro ya tabbatar da mutuwar sojojin Nijar 7 dake cikin dakarun wanzar da zaman lafiya na Onuci dake Cote d'Ivoire a ranar Juma'a, takwas ga watan Yuni ga al'ummar kasa.
Sojojin na sintiri ne a yayin da suka fada cikin wani kwancin bauna na wasu mutanen dake dauke da makamai da ba'a tantance su ba, da sunan shugaban kasa, da gwamnatin kasa da kuma al'ummar Nijar baki daya ya gabatar da ta'aziya da iyalan mamatan da danginsu.
Wannan matsala, ba za ta hana cigaba aikin sojojin kasar Nijar ba, a gaban nauyin dake kan wuyansu na kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali ga 'yan uwan mu na mutanen kasar Cote d'Ivoire, in ji Karidjo.
A nasa bangare, ministan shari'a kuma kakakin gwamnatin Nijar, Marou Amadou ya furta cewa wannan kisa ba za'a rufe ido kansa ba.
Yawan sojojin kasar Nijar dake cikin dakarun tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake a yanzu haka a kasar Cote d'Ivoire ya kai kimanin 900 a cewar wata majiyar sojoji a birnin Yamai. (Maman Ada)