A cikin wani jawabin da ya gabatar ta talabijin din kasar, shugaban hukumar CEI, Youssouf Bakayoko ya nuna cewa bayan kammala ayyukan hukumarsa, jam'iyyar hadin kan 'yan kishin kasa RPR ta samu kujeru 127 bisa 254.
Haka kuma mista Bakayoko ya shaida cewa wannan zabe ya bayyana niyyar al'ummar kasar Cote d'Ivoire na neman zaman lafiya tsakanin kabilun kasar baki daya, kuma zauren majalisar dokokin kasar zai wakilci jam'iyyu daban daban dake kasar.
Mista Bakayoko ya nuna godiyarsa zuwa ga gwamnatin kasar tare da mutanen kasar da kungiyoyi da kasashen duniya dake tallafawa kasar kan kokarin da suka bayar wajen shirya wannan zabe cikin nasara da zaman lafiya.
Daga karshe shugaban hukumar CEI ya nuna cewa kammala wannan zabe shi ne ke tabbatar da girkuwar dimokuradiyya da zaman doka da oda a cikin kasar Cote d'Ivoire.
Ita wannan majalisar dokokin za ta kasance daga shekarar 2011 zuwa 2016 da kujeru 255.
Wannan zabe bai gudana ba a yankin Logouade dake yammacin kasar bayan mutuwar wani dan takara a lokacin yakin neman zabe.
Jam'iyyar PDCI ta Henri Konan Bedie ta zama ta biyu bayan jam'iyyar RDR da kujeru 77.
Sai dai kuma jam'iyyar tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo bata halarci wannan zaben 'yan majalisar dokokin kasar ba.(Maman Ada)