Sojojin Cote d'Ivoire da na MDD sun hada karfinsu domin kiyaye zabubukan kananan hukumomi a kasar
Zabubukan kananan hukumomin na zagon farko sun fara gudana tun ranar Lahadi a kasar Cote d'Ivoire ba tare da wata matsala ba, a cewar wani dan jaridar kamfanin dillancin labarai na Xinhua. A wurare daban daban na kasar, sojojin Cote d'Ivoire da na MDD ne suka dauki niyyar hada karfinsu domin tabbatar da ganin an gudanar tare da kammala wadannan zabubuka cikin adalci da kwanciyar hankali. Yan sanda, da jami'an jandarma da na tawagar sojojin majalisar dinkin duniya dake kasar Cote d'Ivoire (ONUSI) ne aka watsa ko'ina kuma ake ganinsu a manyan yankuna hudu da wadannan zabubuka suka shafa. A cewar magajin garin Ferkessedougou dake arewacin kasar mista Soilio Diakite, ya zama wajibi a dauki matakan tsaro da suka dace domin takatar da duk wasu tashe tashen hankali da za su iyar bullo kai bayan wadannan zabubuka. (Maman Ada)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku