in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Cote d'Ivoire ta dauki niyyar kare jama'arta da dukiyoyinsu a kan hanyoyin kasar
2011-11-21 14:27:37 cri
Ministan gine ginen tattalin arziki na kasar Cote d'Ivoire Patrick Achi ya bayana a ranar Lahadi a birnin Abidjan cewa gwamnatin kasar ta dauki niyyar kara kyautata tsaron jama'a da dukiyoyinsu a kan hanyoyin kasar.

Mista Achi ya fadi haka a lokacin da yake karanta wani jawabin gwamnatin kasar albarkacin bikin ranar kasa da kasa kan tunawa da mutanen da suka mutu a sakamakon hadarin mota tare da gabatar da manyan matakan da za'a dauka domin cimma muradin da aka sanya gaba.

Muradin shi ne yayata umurnonin kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika dake amfani da kudin Sefa wato UEMOA game da batun tsaro kan hanyoyi, daukar nauyin mutanen da hadari ya rutsa da su, ba da horo cikin lokaci ga direbobin dake da kwarewa.

Haka kuma ya kamata a dauki matakan karfafa ba da horo kan batun hanyoyin motoci da tuki a cikin makarantu, gyara tsarin hanyoyin kasar da kuma kulawa da lafiyar motoci in ji ministan.

Kamar sauran kasashen duniya, kasar Cote d'Ivoire ta yi bikin ranar kasa da kasa ta tunawa da wadanda suka kwanta dama dalilin hadarin motoci kan hanya.

A cewar kungiyar kiwon lafiya ta duniya OMS, hadari kan hanyoyi na janyo a kowace shekara mutuwar mutane miliyan 1.3 yayin da miliyan 50 ke jin rauni.

A kasar Cote d'Ivoire, hadarin mota na janyo mutuwar mutane 600 kowace shekara kuma a cikinsu kashi 40 cikin 100 na shafar masu tafiyar kasa.(Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China