Ministan dake kula da harkokin yawon bude ido, Charles Ake Atchimou dake karanta wani jawabin gwamnatin kasar a ranar Litinin a birnin Abidjan ya fayyace cewa kai ziyara ga wasu wurare wata babbar hanya ce ta karuwa da al'adunsu da kara kyautata zaman jituwar al'umma.
"gwamnatin ta yi kira da a rika kai ziyarar gani da ido a yankunan kasar, dake da al'adu iri daban daban da kuma kabilu 60 ta yadda za mu iya sanin juna domin zama tare yadda ya kamata" Mista Atchimou ya kara da cewa.
A cewarsa kuma, al'ummar kasar Cote d'Ivoire tana bukatar zama tamkar tsintsiya madaurinki daya ta yadda za'a cudanya da juna sosai a matsayin wani ginshikin cigaban sha'anin yawon bude ido.
Gwamnatin kasar Cote d'Ivoire tana dukufa ka'in da na'in domin bunkasa sha'anin yawon bude ido na kasar da rikicin siyasa na tsawon watanni biyar ya lalata.(Maman Ada)