ADDR ta samu damar samar da guraben aikin yi ga tsoffin dakaru fiye da dubu 27 cikin dubu 30 da kwamitin kasa kan tsaro ya gabatar mata in ji darektan hukumar Fidel Sarassoro, tare da bitar ayyukan da suka gudanar.
A cewar mista Sarassoro, shirin shigar da tsoffin dakaru a cikin harkokin jama'a da na tattalin arziki na samun babban cigaba sosai. Haka kuma jami'in ya jaddada muhimmancin kara fadakar da tsoffin mayakan bisa damuwarsu game da wannan shiri, da kuma hukumomin yankunan kasar.
Shugaban ADDR ya kuma bayyana cewa ginshikin shirin karbe makamai, tattara tsoffin dakaru da samar masu ayyukan yi shi ne hada kan al'umma.
Bisa majiya mai tushe, shirin karbe makamai da shigar da tsoffin dakaru masu gaba da juna zai lakume biliyan 92 na kudin Sefa kwatankwacin Euro miliyan 140.
Bisa yawan tsoffin mayaka dubu 65, an yi shirin sanya kimanin dubu 30 suka samu aikin yi a karshen shekarar 2013 kana sauran dubu 35 zasu fara aiki a shekarar 2014. (Maman Ada)