A cewar jami'in kula da harkokin babbar ma'aikatar haraji ta kasar, mista Bruno Kanga, wannan aiki ne na samarwa hukumomin karbar haraji wani cibiyar alkaluma da bayanai na gaskiya da zata taimaka wajen tantance yawan manyan 'yan kasuwa dake gudanar da harkokin kasuwanci na cikin kasar baki daya. "Wannan kidaya ta jama'a zata kai ga ba da hanyar bude asusu kyauta na 'yan kasa ga wadannan 'yan kasuwa" in ji mista Kanga, tare da bayyana muhimmancin sanin adadin masu ruwa da tsaki a wannan fanni da kuma yankuna. (Maman Ada)