'Ya dace mu samu wata nagartacciyar manufar diplomasiyya ba wai bisa siyasa kawai ba har ma ta fuskar tattalin arziki domin janyo masu hannu da shuni ta yadda kasar zata komawa hanyar bunkasuwa da cigaba', in ji mista Duncan a yayin wani taron manema labarai bisa rangadin da shugaban kasar, Alhassane Ouattara ya kai a wasu kasashe.
A cikin tsakiyar watan Nuwamba da Disamba, shugaban kasar Cote d'Ivoire ya ziyarci kasashen Benin, Togo, Nijar, Burkina-Faso da Guinee dake shiyyar yammacin Afrika kafin ya isa kasar Belgium.
A ra'ayin ministan harakokin wajen kasar Cote d'Ivoire, wannan rangadi na shugaban kasar na daga cikin tsarin samar da zaman lafiya da tsaro a cikin kasar Cote d'Ivoire da ma shiyyar, baya ga haka da kuma yunkurin sake ingiza tattalin arzikin kasar gaba, da kuma batun sake gina kasar.
' Za'a ga alfanun wannan rangadi a shekara mai zuwa' a cewar mista Duncan dake bada sanarwar zuwan masu zuba jari da dama cikin kasar.(Maman Ada)