Bayan ganawarta tare da firaministan kasar Jeannot Ahoussou Kouado, Madam Arbia ta nuna cewa babban batun da aka tattauna kansa tare da hukumomin kasar shi ne na taimakawa tafiyar da harkokin CPI cikin kasar yadda ya kamata.
Kasar Cote d'Ivoire ta rattaba hannu a cikin watan Fabrairu kan wata yarjejeniya tare da CPI kan matsayi da bada kariya ga ma'aikata da gine ginen kotun dake cikin kasar.
Madam Arbia ta ce, wannan aiki nada muhimmanci wajen baiwa kotun damar tafiyar da harkokinta a duk fadin kasar Cote d'Ivoire da kuma bude wani reshe a wajen birnin Abidjan.
Haka kuma ta kara da cewa, ayyukan da aka gudanar na baya baya sun nuna cewa bude wannan reshen CPI ya zama wajibi domin kula da dangantaka mai karfi tare da hukumomin kasar da ma wasu masu fada a ji a wannan fanni.
An ce, reshen kotun zai taimakawa CPI gudanar da aikinta na shari'a cikin 'yanci ba tare da nuna son kai ba a kasar Cote d'Ivoire da kuma biyan bukatun matso CPI kusa da al'ummomin da tashe tashen hankali da rikicin siyasa ya ritsa da su, musammun ma a fannin manyan laifufukan da suka shafi kotun, da kuma wayar da kan jama'a bisa 'yancin su. (Maman Ada)