A matsayinsa na shugaban gwamnati kana ministan tsaro, tun daga ran 20 zuwa 26 ga wata Soro zai kula da aikin tura shugabannin yankuna na mabambantan sassan rundunonin jamhuriya na Cote d'Ivoire (FRCI), wadda ita ce sabuwar rundunar soji ta kasar, da kuma kafa rundunar 'yan sanda ta kasar.
Wannan aiki na da nufin farfado da yanayin zamantakewar kasar, bayan kwashe shekaru fiye da goma ana rikicin siyasa, wanda ya janyo rabe-rabe a kasar, inda 'yan tawaye ke tafiyar da iko a yankin arewaci, sannan kudanci ke karkashin ikon gwamnati.
Tun bayan da wani yunkurin juyin mulkin gwamnatin Laurent Gbagbo ya ci tura ne a shekara ta 2002 dai, kungiyar New Forces ta mamaye yankin arewacin. A lokacin zaben shugaban kasa na watan Nuwamban shekara ta 2010 kuma kungiyar ta New Forces ta hada gwiwa da Alassane Ouattara, wanda ya ja da Laurent Gbagbo.
Kungiyar ta tsofin 'yan tawayen dake dauke da makamai ta taimakawa Ouattara hawa karagar mulki bayan fatattakar rundunonin dake biyayya ga Gbagbo, wanda ya ki amincewa da shan kashin da ya yi a zaben. (Garba)