in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin majalisun kungiyar G20 sun kirayi a kara yin hadin gwiwa
2013-04-06 16:25:14 cri
A ran Jumma'a 5 ga wata, aka rufe taro karo na 4 na shugabannin majalisun kafa dokoki na kasashe mambobin kungiyar G20 da aka shafe kwanaki 2 ana yinsa a garin Mexico, babban birnin kasar Mexico, inda aka fitar da wata hadaddiyar sanarwa. Bisa wannan sanarwa, an ce, ya kamata bangarori daban daban su kara yin hadin gwiwa kan yadda za a farfado da tattalin arzikin kasa da kasa, yardar al'umma, tallafawa kokarin neman ci gaba, kwantar da halin da ake ciki kan harkokin hada-hadar kudi, samar da guraban aikin yi masu inganci da dai makamatansu.

Wannan sanarwa ta nuna cewa, kaddamar da wannan taro ya bayar da gudummawa ga kokarin neman hanyar warware matsalar tattalin arziki da ake fama da ita a duk duniya. Kana sanarwar ta bukaci mambobin kungiyar G20 da su hanzarta aiwatar da shirin yin gyare-gyare kan yawan kaso na asusun IMF da aka daddale a shekarar ta 2010.

Sannan sanarwar ta yi kira ga bangarori daban daban da su nuna goyon baya ga yarjejeniyoyin da suke da nasaba da sauyin yanayin duniya, ta yadda za a iya tabbatar da samun dawaumammen ci gaba a nan gaba. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China