Zhu Guangyao ya ce, shugabannin kasar Sin sun jaddada sau da dama cewa, Sin na nuna imani cewa, nahiyar Turai na da karfin warware rikicin kudin Euro da karfin kansu, kuma na da karfin warware kalubalen da take fuskanta.
Wata sabuwa kuma, an rufe taron ministocin kudi da shugabannin bankunan tsakiya na kungiyar G20 a wannan rana, inda aka tattauna kan halin tattalin arzikin da duniya ke ciki, da batun kara daidaita tsarin kudi na duniya da sauransu. Daga bisani kuma aka fitar da wata sanarwa bayan taro, inda ta yi maraba da matakan da kasashen Turai suka dauka wajen daidaita ayyukan kudi, magance kalubalen dake cikin kasuwannin kudi, kyautata tsarin kudi, sa kaimi ga kwaskwarima da aka yi wa tsare tsare da zummar samun bunkasuwa, da kuma ba da taimako ga kasar Girka. Ban da wannan kuma sanarwar ta yi kira da a yi wa tsari kwaskwarima a yankin dake yin amfani da kudin Euro cikin hanzari.
An ba da labarin cewa, tawagar kasar Sin ta halarci taron a karkashin jagorancin shugaban bankin jama'ar kasar Zhou Xiaochuan da mataimakin ministan kudi na kasar Zhu Guangyao.(Amina)