in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin duniya na ci gaba da fuskantar kalubalen koma baya
2012-11-06 15:32:51 cri
Daga ran 4 zuwa 5 ga watan nan, an kira taron ministocin kudi da shugabannin manyan bankunan kasashe mambobin kungiyar G20 a birnin Mexico hedkwatar kasar Mexico. Inda suka tattauna kan wasu manyan batutuwa, ciki har da halin da duniya ke ciki a fannin tattalin arziki, tsarin raya kungiyar ta G20 mai karfi da daidaituwa cikin dogon lokaci, kyautata tsarin hukumomin kudi, ba da tabbaci ga tsarin kudin duniya, da kara zuba jari ga aikin kula da makamashi, kayayyaki, da aikin warware batun sauyin yanayi da sauransu. Kuma sun ba da hadaddiyar sanarwar bayan taron.

An ce, ko da yake an dan samu ci gaban wajen farfadowar tattalin arzikin duniya, amma, ana cigaba da fuskantar kalubalen koma baya. Ban da haka, kasashen Turai na fuskantar kalubaloli yayin da suke aiwatar da matakan tinkarar matsalar basuka, kasar Amurka kuma kila ta fuskanci kara tsuke bakin aljihunta. Wannan dai matsala ta shafi wasu kasashe masu tasowa inda suma ke fama da rashin samun karfin bunkasar tattalin arziki, mai yiwuwa ne za a fuskanci matsalar cinikayyar shige da fice ta fuskar manyan kayayyaki. A sa'i daya kuma, kasashe da dama na fuskantar matsalar rashin guraben aikin yi, don haka ya kamata, a tabbatar da daidaito a fannin tattalin arzikin duniya gaba daya.

An ce, ya kamata, bangarori daban-daban na kungiyar G20 su cika alkawarin da suka dauka wajen aiwatar da shirin Los Cabos daga duk fannoni kuma cikin lokaci. (Amina)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China