in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kawo karshen taron koli karo na bakwai na kasashen G20
2012-06-20 16:37:10 cri

An kammala taron koli karo na bakwai na kasashen G20 na kwanaki biyu a ran 19 ga wata a birnin Los Cabos na kasar Mexico, yayin taron, mahalartan kuma shugabannin kasashen G20 sun tattauna kan wasu manyan batutuwa ciki har da halin tattalin arzikin duniya, kara inganta tsarin kudi na duniya da samar da guraben aikin yi. Haka kuma sun tattauna batun neman samun bunkasuwa, ciniki da sauransu. Sannan daga baya aka fitar da sanarwar taron koli na Los Cabos na G20.

Sanarwar ta bayyana cewa, abin da G20 ta sa gaba shi ne, neman samun bunkasuwa mai dorewa yadda ya kamata. Kasashen G20 za su yi iyakacin kokarinsu wajen habaka bukatu da karfafawa juna gwiwa, tare kuma da samar da guraben aikin yi ta hanyar kokarin bunkasa tattalin arziki da kara azama ga aikin kudi a duniya. Abin da ya sa, aka zartas da shirin neman samun bunkasuwar tattalin arziki da samar da guraben aikin yi na Los Cabos.

Game da batun kara zubawa IMF kudi, sanarwar ta ce, mahalartan taro sun fahimci wajibcin kafa tsarin tabbatar da zaman lafiya a kasa da kasa da na shiyya-shiyya. Har ila yau, mahalartan taron sun yi alkwarin karazubawa IMF kudi da yawansu zai kai dala biliyan 450.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China