in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An rufe taron ministocin kudi da shugabannin bankunan G20
2013-02-17 15:45:07 cri

A ranar 16 ga watan nan ne aka rufe taron ministocin kudi da shuwagabannin bankunan kungiyar kasashe 20 masu karfin arziki ta G20.

Hadaddiyar sanarwar bayan taron cewa, yanzu, duniya na fama da koma bayan tattalin arziki, tare kuma da fuskantar kalubaloli da hadarori da dama.

Taron na ganin cewa, da farko, tinkarar kalubalolin da ake fuskantar, na bukatar kasashe masu wadata su tsai da managarcin tsarin kyautata hada-hadar kudade cikin matsakaici ko dogon lokaci mai amfani, haka kuma manufofin kudi da suke dauka su dace da matakin da ake bi wajen tabbatar da farashin kayayyaki cikin tsanaki, da farfadowar tattalin arzikinsu.

Bugu da kari, kamata ya yi, kasashe daban-daban su tabbatar da alkawarin da suka yi, dangane da kyautatuwar hukumomin kudi da tsare-tsare, tare kuma da daidaito tsakanin kayayyaki, da samar da su gwargwadon bukata, ta yadda za a farfado da tattalin arzikin duniya ba tare da wani bata lokaci ba.

A sa'i guda, ana fatan ci gaba da ba da tabbaci ga tsarin darajar musayar kudi, da kuma yaki da rage darajar kudi bisa mugun buri, dama kin yarda da manufar kariyar cinikayya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China