Ministan kudi na Rasha ya bayyana cewa, a matsayinta na kasar dake rike da mulkin kungiyar G20 a bana, Rasha na ganin cewa, kamata ya yi kasa da kasa su yi kokari kan sa kaimi ga zuba jari, tabbatar da samar da haske a cikin kasuwanni da kara amincewa da juna, da kuma kara kokarin sarrafa kayayyaki.
Ya ce, ban da yin kwaskwarima kan tsarin kudaden duniya da sauransu, Rasha tana dora muhimmanci kan neman bashi tsakanin juna, kulawa da bashin kasa da kasa da dai sauransu a taron kungiyar G20 na bana.
Shugaban bankin duniya, Jim Yong Kim ya bayyana cewa, ko da yake yanzu matsalar kudi ta duniya ta riga ta samu kyautatuwa, wajibi ne kasa da kasa su yi kokarin sa kaimi ga tabbatar da zaman lafiya da bunkasa tattalin arziki a nan gaba. A ganinsa, kungiyar G20 ta kasance wata muhimmiyar dandali yin shawarwari kan manufofin tattalin arziki tsakanin kasashe masu sukuni da kasashe masu karfin bunkasar tattalin arziki.
A nasa bangare kuma, shugaban baitul-malin Amurka, wato FED, Ben Bernanke ya furta cewa, kasa da kasa sun kasance cikin wannan tsarin hada-hadar kudi na duniya baki daya shi ne ya sa jari ke iya tafiya daga wata kasa zuwa wata kasa ta daban cikin sauki. A sabili da haka, dole ne a samu daidaito tsakanin kasa da kasa a fannin tsarin hada-hadar kudi.(Fatima)